Tarayyar Afrika Ta Yabawa Mutane Da Gwamnatin Kasar Gambia Kan Zabe
(last modified Mon, 05 Dec 2016 16:59:23 GMT )
Dec 05, 2016 16:59 UTC
  • Tarayyar Afrika Ta Yabawa Mutane Da Gwamnatin Kasar Gambia Kan Zabe

Kungiyar tarayyar Afrika ta yabawa mutane da gwamnatin kasar Gambia kan gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya.

Kamfanin dillancin labaran Xinhuwa na kasar China ya nakalto rahoton da shugaban kungiyar tana fadar haka a wani rahoton da ta fitar a yau litinin.

Delomini Zuma shugaban kungiyar ta AU ta kara da cewa mutanen kasar Gambia sun nuna bajinta kan yadda suka gudanar zabe cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali, sannan ta yabawa shugaban kasa mai ci Yahayah Jami kan rawan da ya taka wajen ganin an gudanar da zaben cikin aminci da kuma tsarin democradia. Banda haka kungiyar ta Au tace tana taya Adama Baro kan zabensa da aka yi ta kuma kara da cewa a shirye take ta yi aiko da sabuwar gwamnatin da aka zama, 

A ranar Jumma'an da ta gabata ce hukumar zaben kasar Gambia ta bayyana sakamakon zaben shugaban kasa wanda aka gudanar a ranar Alhamis inda sakamakon ya nuna cewa Adama Barow na gamayyar Jam'iyyun adawa ne suka lashe zaben tare da samun 45.5%. a yayin da shugaba mai ci ya zo na biyu da kashi 33.6%.