Kokarin tabbatar da yarjejjeniyar Sulhu a kasar Mali
Shugaban kasar Mali ya tattauna da wakilan kungiyoyin 'yan tawaye domin daukan matakan da ya kamata na gudanar da yarjejjeniyar sulhun da aka cimma a kasar
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa a marecen jiya Lahadi Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Kieta ya tattauna da wakilan kungiyoyin dake dauke da makamai masu goyon bayan yarjejjeniyar sulhun da aka cimma da masu adawa da ita dake arewacin kasar, wannan tattaunawa dai ta meda hankali ne kan yadda za a gaggauta zartar da yarjejjeniyar sulhun da aka cimma tsakanin Gwamnati da kungoyoyin 'yan tawayen kasar.
A karshen tattaunawar Ibrahim Boubacar kieta ya shaida manema labarai cewa an samu ci gaba a wannan tattaunawa tare da tsayar da ranar 19 ga watan Maris mai kamawa domin ci gaba da wannan tattaunawa.
Har ila yau Shugaban kasar ta Mali ya bayyana cewa nan da watani biyu masu zuwa za su dauki matakin da ya dace domin karfafa matakan tsaro a arewacin kasar.
Ya zuwa yanzu kwamitin da aka kafa na zartar da yarjejjeniyar sulhu da aka cimma da ya kuma ya kumshi wakilan gwamnati gami da kungiyoyin 'yan tawaye ya zauna har so biyar ba tare da ya cimma wata matsaya ta a zo a gani ba.
Idan ba a manta ba dai a ranar 15 ga watan yulin na shekarar da ta gabata ne, bayan gudanar da tattaunawa da dama tsakanin Gwamnatin Mali da 'yan tawayen arewacin kasar, suka cimma yarjejjeniyar sulhu bisa shiga tsakanin kasar Aljeria.