An tabbatar da Hukuncin rusa matakin baiwa Saudiya tsibiran Masar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i14896-an_tabbatar_da_hukuncin_rusa_matakin_baiwa_saudiya_tsibiran_masar
Majalisar Mashawarta ta Alkalan Masar ta bukaci Gwamnati da yaga yarjejjeniyar da ta cimma da Gwamnatin Saudiya na Bata tsibiran Tiran da Sanafir.
(last modified 2018-08-22T06:59:21+00:00 )
Dec 06, 2016 02:16 UTC
  • An tabbatar da Hukuncin rusa matakin baiwa Saudiya tsibiran Masar

Majalisar Mashawarta ta Alkalan Masar ta bukaci Gwamnati da yaga yarjejjeniyar da ta cimma da Gwamnatin Saudiya na Bata tsibiran Tiran da Sanafir.

Jaridar Alkudusul-Arabi ta habarta cewa Majalisar Mashawartan alkalan Masar sun fitar da wani rahoto inda a cikin sa suka bayana cewa dalilai da shaidu sun tabbatar da cewa tsibiran Tiran da Sanafir mallakin kasar Masar ne don haka yarjejjeniyar da Gwamnatin Masar ta cimma da masarautar Saudiya na mayar da tsibiran ga Saudiya ba zai yi wani tasiri ba.

Daga cikin dalilan da Majalisar ta gabatar, mu'amalar da Saudiya ta yi da wadannan tsibirai cikin shekarun da suka gabata shike tabbatar da cewa tsibiran mallakin kasar Masar ne, kuma a yayin da Haramcecciyar kasar Isra'ila ta mamaye su daga shekarar 1956 zuwa 1967 Sojojin Masar suka yi kokari wajen 'yanto su, daga wancan lokaci babu wani martani da saudiyar ta mayar dangane da hakan.

A jiya litinin ne kotun kolin ta Ma'aikatun kasar ta gudanar da zama domin yin nazari kan bukatar da kungiyar alkalan kasar suka gabatar na ta yi watsi da hukuncin Gwamnati na baiwa Saudiya tsibiran Tiran da Sanafir, a karshen zaman kotun ta amince da bukatar alakan kasar.

A farkon watan Avrilun da ya gabata ne aka cimma yarjejjeniyar baiwa Saudiya tsibiran Tiran da Sanafir yayin da sakin salman bin Abdul-Aziz na saudiya ya kai ziyara birnin Alkahira, lamarin da ya fuskantar martani mai tsanani daga bangare masu adawa da hakan.