An gano Makaman Fasakwauri A Tsakanin Iyakokin Kasashen Aljeriya Da Mali.
Dec 06, 2016 08:37 UTC
Gano da Kame Makamai A kan iyaka da Mali
Ma'aikatar tsaron Aljeriya ta sanar da gano makaman fasa kwauri a gundumar Adrar da ke kan iyaka da kasar Mali.
Kamfanin dillancin labarun Xinhua na kasar Sin ya ambato ma'aikatar tsaron kasar ta Aljeriya tana cewa; Jami'an da su ke kula da kan iyaka ne su ka gano makaman, da kuma kame su.
Aljeriya dai ta aike da dubban sojojinta zuwa kan iyakokinta da Mali da kuma Libya domin hana kungiyoyi masu dauke da makamai shiga cikin kasar. Kuma tun daga 2015 zuwa yanzu, an kame makamai da kuma 'yan ta'adda masu yawan gaske akan iyakokin.
Tags