Majalisar Dinkin Duniya Za ta ci gaba Da Taimakakwa Kasar Ghana.
Bayan Zabe, majalisar dinkin duniya za ta taimakawa kasar Ghana.
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Bon Ki Moon ya fitar da bayani da aciki ya jinjinawa hukumar zaben kasar Ghana, saboda nasarar gudanar da manyan zabuka cikin nasara.
Bon Ki Moon ya kuma ce Majalisar Dinkin Duniyar za ta ci gaba da taimakawa kasar ta Ghana domin ganin cewa an ci gaba da kare tsarin demokradiyya.
Bugu da kari, Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniyar, ya jinjinawa shugaban kasar John Dramani Mahama saboda rawar da ya taka wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya alokacin zabukan, sannan kuma ya yi wa Nana Akufo Ado, murnar lashe zaben shugaban kasar.
Akufo Ado, ya sami kaso 53% na jumillar kuri'un da aka kada a kasar ta Ghana, abinda ya maida shi zama wanda ya lashe, zaben, kaan shugaban kasa mai ci Mahama.