Rahotanni: Mutane 3 Sun Mutu Wasu Sun Raunana, A Harin Maiduguri
Rahotanni daga birnin Maiduguri, babban birnin jihar Bornon Nijeriya na nuni da cewa alal akalla mutane 3 sun mutu kana wasu da dama sun sami raunuka sakamakon fashewar wasu abubuwa guda biyu a garin na Maiduguri.
Kafar watsa labaran nan ta Premium Times ta nakalto wani jami'in kungiyar 'yan sa kai na JTF na garin Bello Danbatta yana cewa an tabbatar da mutuwar mutane uku din sannan wasu da dama kuma sun sami raunuka sakamakon wannan harin da aka kai Maidugurin a yau Lahadi.
Jami'in ya kara da cewa: Harin na kunar bakin wake ne, sai dai har ya zuwa yanzu ba a riga da an tantance yadda lamarin ya faru da kuma yawan wadanda abin ya shafa ba.
Shi ma a nasa bangaren, kakakin hukumar agaji ta gaggawa ta Nijeriyan NEMA,Sani Datti ya ce mutane ukun da suka mutum 'yan kunar bakin waken ne wadanda mata ne da suka kai harin, sannan kuma sauran mutane 17 kuma da suka sami rauni mutanen gari ne wadanda tuni aka kai su asibitocin birnin na Maiduguri don kula da su.
Kafar watsa labaran ta Premium Times ta ce harin da ya faru ne da misalin karfe 8:48 na safiyar yau a wani waje da jama'a suke tare kusa da babbar kasuwar birnin na Maiduguri.