Adadin Mutanan da suka rasu ya karu sanadiyar tashin Bam a Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i15148-adadin_mutanan_da_suka_rasu_ya_karu_sanadiyar_tashin_bam_a_somaliya
Adadin Mutanan da suka rasu sanadiyar tashin Bam a birnin magadushu na kasar Somaliya ya haura zuwa 35
(last modified 2018-08-22T11:29:23+00:00 )
Dec 12, 2016 05:20 UTC
  • Adadin Mutanan da suka rasu ya karu sanadiyar tashin Bam a Somaliya

Adadin Mutanan da suka rasu sanadiyar tashin Bam a birnin magadushu na kasar Somaliya ya haura zuwa 35

Kafar watsa labaran Alyaumu-Sabi'i na kasar Masar ya nakalto Jami'an 'yan sanadar Somaliya na cewa  adadin Mutanan da suka rasu sanadiyar tarwatsewar Motar da aka makile ta da Bama-bami a babbar tashar ruwan kasar  jiya Lahadi ya haura zuwa 35 yayin da wadanda suka jikkata ya haura zuwa 50.

Duk da cewa har yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai hari, to amma ana zarki kungiyar ta'addancin nan ta Ashabab mai alaka kut da kuta da kungiyar Alka'ida, kuma kungiyar Ashabab din ta sha bayyana cewa tana kai irin wadannan hare-hare ne da nufin yakar Gwamnatin dake samun goyon bayan kasashen Yamma.