An tabka Magudi a zaben Gambia
Jam'iya mai millki ta kasar Gambia ta zarki Kwamitin zabe da tabka magudi a zaben shugaban kasa.
A cikin wata sanarwa da ta fita a jiya Lahadi, Jam'iyyar da shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh ya tsaya takara ta ce shugaban kasar zai garzaya kotun koli don kalubalantar sakamakon zaben, saboda sun gano magudin da hukumar zaben kasar ta yi. tun da farko dai Hukumar zaben kasar ta sanar da dan takaran jam'iyyar adawa Adama Barrow a matsayin wanda ya lashe zaben.inda Shugaba Jammeh ya amince da shan kaye har ya taya Mr Barrow murnar lashe zaben.
Sai dai a wani jawabi na ba zata da yayi ranar juma'ar da ta gabata, shugaban ya ce sam ba zai amince da sakamakon zaben ba, saboda an tabka magudi a cikin sa,matakin da ya janyo kakkausar suka daga Majalisar Dinkin Duniya da kuma kungiyar tarayyar Afrika.
Wata sanarwa da Shugabar kungiyar tarayyar Afrika Dlamini-Zuma ta fitar, ta yi kira ga Shugaba Jammeh da ya tabbatar ya bayar da hadin kai wurin mika mulki ga sabuwar gwamnati cikin lumana.ita ma Amurka ta nuna takaicinta kan yadda shugaban mai barin gado ya sauya matsaya kan sakamakon zaben.
A shekarar 1994 dai Yahya Jameh ya dare kan karagar milkin kasar ta gambia, bayan juyin mulkin da ya jagoranta a kasar.