Buhari Ya Kirayi Al'ummar Nijeriya Da Su Kara Hakuri Da Gwamnatinsa
Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya kirayi 'yan kasar da kada su yanke kauna dangane da karfin da gwamnatinsa take da shi na kyautata rayuwarsu, yana mai cewa kasafin kudin shekara ta 2017 da ya gabatar na dauke da matakan da za su iya fitar da kasar daga cikin matsalar karayar tattalin arziki da ake fuskanta.
Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne cikin sakon Maulidi don tunawa da ranar haihuwar Ma'aiki (s) da ya aike wa al'ummar kasa inda ya ce musu kada su damu don kuwa gwamnatinsa tana iyakacin kokarinta wajen magance matsalar tattalin arzikin da ake fuskanta a kasar musamman irin matakan da aka dauka cikin kasafin kudin shekara ta 2017 da zai gabatar wa 'yan majalisar kasar a jibi Laraba.
Shugaba Buhari ya taya allahirin al'ummar musulmi murnar ranar haihuwar Ma'aiki (s) din inda ya ce Nijeriyan ta amfana sosai daga koyarwar Ma'aiki (s) musamman bangarorin da suka shafi zaman tare cikin kwanciyar hankali, karimci, sadaukarwa, gaskiya da rikon amana wajen ciyar da kasar gaba.
A Nijeriyan a yau 12 ga watan Rabi'ul Awwal ne ake gudanar da bukukuwan Maulidi din don tunawa da ranar da bisa wasu riwayoyi aka haifi Manzon Allah (s).
Gwamnatin Tarayyar Nijeriyan dai ta ba da hutu a yau din a duk fadin kasar don ba wa musulmi daman gudanar da bukukuwan Maulidin.