Shugaban Hukumar Zaben Gambiya Ya Ja Kunnen Shugaba Jammeh
(last modified Tue, 13 Dec 2016 11:11:20 GMT )
Dec 13, 2016 11:11 UTC
  • Shugaban Hukumar Zaben Gambiya Ya Ja Kunnen Shugaba Jammeh

Shugaban hukumar zaben kasar Gambiya Alieu Momarr Njai ya ja kunnen shugaban kasar Yahya Jammeh dangane da kin amincewa da sakamakon zaben shugaban da yayi yana mai cewa hakan ba zai sauya hakikanin lamarin cewa ya sha kaye a zaben shugaban kasar da aka gudanar ba.

Shugaban hukumar zaben na Gambiya ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da kamfanin dillancin labaran Reuters inda ya ce ko da shugaba Jammeh ya je kotu kamar yadda ya ce zai yi, to kuwa ba zai yi nasara ba don kuwa muna da hujjojin da ke tabbatar da ingancin abin da muka sanar a matsayin sakamakon zaben.

A ranar Asabar din da ta gabata ce shugaba Jammeh wanda ya sha kaye a zaben shugaban kasar ya sanar da cewa zai kalubalanci sakamakon zaben a kotun koli ta kasar yana mai zargin cewa an tabka magudi a yayin zaben da aka gudanar; lamarin da 'yan adawar kasar suka yi watsi da shi suna masu cewa ba za su taba amincewa da wani abu ba face mika mulki ga zababben shugaban kasar Adama Barrow.

A bangare guda kuma kungiyar lauyoyin kasar Gambiyan sun shigo sahun masu kiran shugaba Yahya Jammeh da ya girmama sakamakon zaben suna masu bayyana abin da ya ke kokarin yi a matsayin cin amanar kasa.