Shugaba A/Kudu, Zuma Ya Tsallake Kokarin Tsige Shi A Majalisar Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i1531-shugaba_a_kudu_zuma_ya_tsallake_kokarin_tsige_shi_a_majalisar_kasar
Shugaban kasar Afirka ta kudu Jacob Zuma ya tsallake wani kokari na tsige shi a yayin kuri’ar nuna rashin amincewa da gwamnatinsa da aka kada a majalisar dokokin kasar a jiya Talata saboda abin da babbar jam'iyyar adawa ta kira siyasarsa da ke cutar da tattalin arzikin kasar.
(last modified 2018-08-22T11:27:53+00:00 )
Mar 02, 2016 05:27 UTC
  • Shugaba A/Kudu, Zuma Ya Tsallake Kokarin Tsige Shi A Majalisar  Kasar

Shugaban kasar Afirka ta kudu Jacob Zuma ya tsallake wani kokari na tsige shi a yayin kuri’ar nuna rashin amincewa da gwamnatinsa da aka kada a majalisar dokokin kasar a jiya Talata saboda abin da babbar jam'iyyar adawa ta kira siyasarsa da ke cutar da tattalin arzikin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ce shugaba Zuma, wanda yake da goyon bayan jam'iyyar ANC mai mulki wacce kuma take da kusan kashi biyu cikin uku na kujerun majalisar, ya samu kuri’u 225 akan kuri'a 99 da suka nuna goyon bayansu ga kudurin tsige shi kana wasu 22 kuma suka ki kada kuri'arsu.

Wannan dai shi ne karo na biyu cikin shekara guda, da 'yan majalisar dokokin Afrika ta Kudun ke kada kuri’ar yunkurin tsige shugaba Zuman sakamakon zarginsa da aikata laifin cin hanci da rashawa bugu da kari kan rikon sakainar kashi ga tattalin arzikin kasar.

Jam’iyyar ‘yan adawa ta Democratic Alliance ce ta bukaci a gudanar da kuri’ar yunkurin tsige shugaba Zuma kamar yadda shugabanta Mmusi Maimane ya ce hakan ita ce hanyar mafi dacewa ta tsige shugaba Zuman wanda ke da alhakin tarbarbarewar tattalin arzikin kasar, lamarin da jam’iyyar ANC mai mulki ta ce yin karen tsaye ne ga tsarin demokradiyya na kasar.