Somaliya: Ci Gaba Da Hare-haren 'Yan ta'adda
Wata Mota Mai Makare Da Bama-bamai ta tarwatse A Kusa Da Fadar Shugaban Kasa
Majiyar 'yan sanda a kasar Somaliya ta ce; motar da ta ke makare da bama-bamai ta tarwaste ne a wani wuri mai nisan mita 500 daga fadar shugaban kasa a birnin magadishu.
Wani jami'in 'yan sanda ya fadawa kamfanin dillancin labarun Reuters cewa; wanda ya kai harin ya tashi motar ne bayan da 'yan sanda su ka tsaida shi a wani wurin bincike.
A cikin kwanaki biyu kadai, an kai hare-haren ta'addancin har sau uku a cikin babban birnin kasar wanda ya ci rayuka da jikkata mutane 100. Sabbin hare-haren dai sun dawo da tsoro a cikin mazauna birnin magadishu.
kungiyar al-shabab dai tana kai hare-hare ne a cikin kasar Somaliya da zummar kifar da gwamnati. Kawo ya zuwa yanzu dai dubban mutane ne hare-haren su ka kashe a cikin kasar da kuma makwabta.