Somaliya: Ci Gaba Da Hare-haren 'Yan ta'adda
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i15322-somaliya_ci_gaba_da_hare_haren_'yan_ta'adda
Wata Mota Mai Makare Da Bama-bamai ta tarwatse A Kusa Da Fadar Shugaban Kasa
(last modified 2018-08-22T06:59:24+00:00 )
Dec 15, 2016 15:55 UTC
  • Somaliya: Ci Gaba Da Hare-haren 'Yan ta'adda

Wata Mota Mai Makare Da Bama-bamai ta tarwatse A Kusa Da Fadar Shugaban Kasa

Majiyar 'yan sanda a kasar Somaliya ta ce; motar da ta ke makare da bama-bamai ta tarwaste ne a wani wuri mai nisan mita 500 daga fadar shugaban kasa a birnin magadishu.

Wani jami'in  'yan sanda ya fadawa kamfanin dillancin labarun Reuters cewa; wanda ya kai harin ya tashi motar ne bayan da 'yan sanda su ka tsaida shi a wani wurin bincike.

A cikin kwanaki biyu kadai, an kai hare-haren ta'addancin har sau uku a cikin babban birnin kasar wanda ya ci rayuka da jikkata mutane 100. Sabbin hare-haren dai sun dawo da tsoro a cikin mazauna birnin magadishu.

kungiyar al-shabab dai tana kai hare-hare ne a cikin kasar Somaliya da zummar kifar da gwamnati. Kawo ya zuwa yanzu dai dubban mutane ne hare-haren su ka kashe a cikin kasar da kuma makwabta.