Al'ummar kasar Zimbabwe na cikin zullumi na barkewar rikicin Siyasa a kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i15442-al'ummar_kasar_zimbabwe_na_cikin_zullumi_na_barkewar_rikicin_siyasa_a_kasar
Maganar Siyasa ta dauki hankalan Al'ummar kasar Zinbabwe bayan da Jam’iyyar Zanu-PF mai mulki ta amince da Robert Mugabe mai shekaru 92 a matsayin dan takarar Jam'iyar na zaben Shugaban kasa na 2018.
(last modified 2018-08-22T06:59:25+00:00 )
Dec 18, 2016 14:47 UTC
  • Al'ummar kasar Zimbabwe na cikin zullumi na barkewar rikicin Siyasa a kasar

Maganar Siyasa ta dauki hankalan Al'ummar kasar Zinbabwe bayan da Jam’iyyar Zanu-PF mai mulki ta amince da Robert Mugabe mai shekaru 92 a matsayin dan takarar Jam'iyar na zaben Shugaban kasa na 2018.

Kafar watsa labaran Afirka News ya habarta cewa, tun bayan da  Jam’iyyar Zanu-PF mai mulki ta amince da tsayawar takarar Shugaban kasar mai ci Robert Mugabe mai shekaru 92 a zaben 2018, sabani tsakanin kungiyoyi da Jam'iyun siyasa ke kara karuwa, A cikin 'yan kwanakin nan Birnin Harare fadar milkin kasar da wasu manyan buraren kasar sun fuskanci Zanga-zanga na Matasan da suke nuna rashin amincewar su kan halin da kasar ke ciki a yanzu, saidai a masu bangare Jami'an 'yan sanda sun yi amfani da karfi wajen kalubalantar masu zanga-zangar.

Tun a shekarar 1980 Shugaba Robert Mugabe ke jan ragamar mulkin kasar Zimbabwe, bayan samun ‘yan cin kan kasar daga turawan milkin mallaka na kasar Birtaniya.

A wannan shekarar dai Mugabe ya fuskanci matsin lambar neman ya sauka daga mukaminsa, sakamakon halin da tattalin arzikin kasar ya tsinci kansa, sai kuma zargin aikata cin hanci da karbar rashawa da ake yiwa jiga jigan gwamnatinsa.