Harin ta'addanci a kudancin Somaliya
Akalla Mutane 9 ne suka rasu sanadiyar harin ta'addanci na kungiyar Ashabab a kudancin Somaliya.
Kamfanin dillancin Labaran Irna na kasar Iran ya nakalto Ahmad Muhamad babban Jami'in tsaron Somaliya na cewa harin ta'addancin da mayakan Ashabab suka kai garin Kisamayu na yankin Juba Assufla dake kudancin kasar yayi sanadiyar mutuwar mutane akalla 9 tare da jikkata wasu da dama na daban.
Ahmad Muhamad ya kara da cewa a yayin wannan hari Jami'an tsaro da na sa kai sun samun nasarar hallaka mayakan 'yan ta'addar na Ashabab guda uku, kuma a halin da ake ciki, ana ci gaba da bincike domin gano wadanda harin ya ritsa da su.
A bangare guda, Dakarun tsaron Somaliyan sun kai farmaki garin Janalah dake yankin Shabily na kudancin birnin Magadushu tare da samun nasarar hallaka mayakan Ashabab kimanin 12.
A baya dai kungiyar ta Ashabab ta mamaye yankunan tsakiya da kuma kudancin kasar ta Somaliya, a shekarar 2012 kungiyar ta yi mubaya'a ga kungiyar ta'addancin nan ta Alka'ida, bayan shigar Rundunar wanzar da zaman Lafiya ta kasashen Afirka, an samu nasarar fatattakar mayakan Ashabab din daga yankunan da dama na cikin kasar, inda yanzu kawai ya rage a kalkashin mamayar su wasu yankuna na kauyen kudancin kasar.