An Kashe Wani Dan Kungiyar Ikhwanul Muslimin A Kasar Masar
(last modified Mon, 19 Dec 2016 18:22:23 GMT )
Dec 19, 2016 18:22 UTC
  • An Kashe Wani Dan Kungiyar Ikhwanul Muslimin A Kasar Masar

Jami'an tsaro a kasar Masar sun kashe dan wata kungiya wacce ake kira Hasm a yayin musayar wuta da su a birnin alkahira na kasar

Tashar television ta Sky News larabci ta nakalto ministan cikin gida na kasar ta Masar yana fadar haka a yau Litinin ya kuma kara da cewa, jami'an tsaron kasar ne suka kai sumame a wani gida mallakin yayan wannan kungiyar wacce ake zatom reshe ne na Ikhwanul muslimin a yankin Jiza na gabacin Alkahira, sun kuma yi musayar wauta da magoya bayan wannan sabuwar kungiyar ta Hasm, sun kashe mutum guda sun kuma gano makamai da boma bomai a gidan, sannan suma jami'an tsaro sun rasa jami'i guda.