An Kashe Sojan Majalisar Dinkin Duniya A Kasar Congo
Majalisar dinkin duniya ta sanar da kashe daya daga cikin sojojinta masu gudanar da ayyukan wanzar da sulhu da zaman lafiya a jamhuriyar dimokradiyyar Congo.
A cikin wani bayani da ya fitar ajiya, babban sakataren majalisar dinkin duniya mai barin gado Ban Ki Moon ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya bayyana cewa wannan babban abin bakin ciki ne kuma abin yin Allawadai.
Ban Ki Moon ya ce dole ne gwamnatin Congo ta dauki matakan da suka dace domin tabbatar da cewa an gano wadanda suka aikata wanann laifi domin su fuskanci shari'a.
A jiya ne aka yi dauki ba dadi tsakanin jam'ian tsaron kasar Congo da sojojin majalisar dinkin duniya ke rufa wa baya da kuma gungun wasu masu dauke da makamai, inda aka kashe daya daga cikin jami'an majalisar dinkin duniya, da kuma wasu masu dauke da makami su biyar, sai kuma wani dan sandan kasar ta Congo guda daya.