Wasu Sun Rasa Rayukansu Sakamakon Rikicin Da Ya Barke A Kongo
Rahotanni daga Jamhuriyar Demokradiyar Congo na cewa alal akalla wasu fararen hula su biyu sun rasa rayukansu kana wasu sun sami raunuka sakamakon bude wuta da sojoji suka yi kan mutanen da suke ci gaba da zanga-zangar nuna adawa ga shugaba Joseph Kabila na kasar.
Rahotannin sun ce rikici ya barke a manyan birane biyu na kasar Demokradiyyar Kongon a yau Talata bayan da shugaban 'yan hamayyar kasar Etienne Tshisekedi ya kirayi al'umma da kada su yarda da shugabancin shugaba Kabilan bayan karewar wa'adin mulkinsa.
Jami'an tsaron sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga-zangar da suka fito kan titunan babban birnin kasar, Kinshasa suna kiran shugaba Kabilan da ya sauka daga karagar mulkin, lamarin da ya sanya jami'an tsaron bude wuta a wasu wajajen sakamakon ci gaba da kone-kone da matasan suke yi.
Wannan rikicin dai yana zuwa ne bayan karewar wa’adin mulkin shugaba Kabila a ranar Lahadin da ta gabata amma ya ki sauka daga karagar mulkin saboda rashin gudanar da zabe da aka yi abin da 'yan adawan suka ce ba za su amince da shi ba don kuwa hakan wani kokari ne na shugaba Kabilan na yin tazarce.