Majalisar Kasar Tunisia Ta Kira Taron Gaggawa Don Tattauna Batun Kisan محمدالزواری
Majalisar dokokin kasar Tunisia ta kira taron gaggawa don tattauna batun kisan inginiyan jiragen sararen samania kasar Mohammad Alzawari.
Tashar televidion ta Almayadeen ta bayyana cewa majalisar dokokin kasar Tunisia ta bada sanarwan gudanar da zaman gaggawa kan kisan da aka yi wa Mohammad Azzawari, wanda ya kasance injiniyar jiragen sama ne kuma yana taimakawa kungiyar Hamas wacce take ta Palsdinu wajen kera jaragen sama narasa matuki.
A ranar Alhamis da ta gabata ce wasu yan bindiga suka harbe Mohammad Azzawari a garin Safafis daga kudancin kasar kuma hanyanzun ba'a bada sanarwan wanda ya kashe sna.
Yan majalisar dai dun bukaci ministan harkokin waje da kuma ministan harkokin waje n kasar da su zo zauren majalisar a gobe jumma'a don bada karin bayani kisan Muhammad Azzawari.
Wasu masana suna ganin mai yuwa HKI ya kasance tana da hannu cikin kisan na Muhammad Azzari.