Demokradiyyar Congo: 'Yan sanda Sun Kame Mutane Da Dama
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i15619-demokradiyyar_congo_'yan_sanda_sun_kame_mutane_da_dama
A jiya alhamis jami'an tsaro a kasar Demokradiyyar Congo Sun kame mutane da dama da su ka shiga Zanga-zanga.
(last modified 2018-08-22T06:59:26+00:00 )
Dec 23, 2016 02:20 UTC
  • Demokradiyyar Congo: 'Yan sanda Sun Kame Mutane Da Dama

A jiya alhamis jami'an tsaro a kasar Demokradiyyar Congo Sun kame mutane da dama da su ka shiga Zanga-zanga.

A jiya alhamis jami'an tsaro a kasar Demokradiyyar Congo Sun kame mutane da dama da su ka shiga Zanga-zanga.

Kamfanin Dillancin Labarin Reuters ya nakalto cewa a yayin Zanga-zangar da aka yi a birnin Kinshasha, domin nuna kin jinin tazarcen shugaba Joseph Kabila, an kame mutane 275.

Rahoton ya ci gaba da cewa; An sami zangi-zanga a cikin garuruwa daban-daban na kasar wacce ta juye zuwa tashin hankali.

 Tuni dai gwamnatin kasar ta hana yin Zanga-zanga a cikin fadin kasar baki daya.

A bisa dokokin kasar ta demokradiyyar congo shugaban kasar ba shi da hakkin tsayawa takara karo na uku idan wa'adinsu biyu kare.