Mali : Sojojin MDD 6 Suka Mutu Bayan Motar Su Ta Taka Nakiya
Rahotanni daga kasar mali na cewa sojojin MDD shida ne suka rasa rayukan su, kana wasu biyu sukaji munanan raunuka bayan da motar su ta taka nakiya a arewacin kasar.
kamar yadda tawagar MDD ta (Minusma) a wannan kasa ta sanar ta ce lamarin ya auku ne a ranar talata data gabata a bisa hanyar Aguelhok zuwa Tessalit a arewacin Kidal.
koda yake sanarwar bata fayace asalin 'yan wace kasa ce lamarin ya shafa, aman ta ce ko a ranar Litinin data gabata irin wannan hadarin ya auku ba tare da raunana kowa ba.
A wata sanarwa data fitar MDD tayi allawadai da wannan al'amari da a cewar ta wasu bata gari keyi da nufin wargaza yunkurin wanzar da zamen lafiya da ake ta kokarin samarwa a arewacin wannan kasa ta Mali.
Tawagar MDD a Mali wato Munusma dake jibge tun a watan Yuli shakara 2013 ta kunshi sojoji da 'yan sanda 11,700.