Firaministan Libiya Ya Kai Ziyara Aljeriya
Firaministan Libiya Fayez al-Saraj, ya ziyarci kasar Aljeriya, inda ya gana da manyan jami'an kasar, a wani mataki na bunkasa yunkurin da ake yi na magance matsalolin tsaro, da wanzar da zaman lafiya a kasar ta Libiya.
Mista Al-Seraj ya shaidawa 'yan jaridu cewa, ziyayar aikin, ci gaba ce kan tattaunawar da sassan biyu ke yi domin ganin sun fidda Libiya daga rikicin siyasar dake addabar ta tsawon shekaru sama da biyar.
Ya ce ya zama wajibi ya jinjinawa rawar da Aljeriya ke takawa, wajen tallafawa gwamnatin hadin kan kasa dake jagoranci a Libiya, yana mai fatan kara tattaunawa da mahukuntanta kan wasu hanyoyi na kawo karshen rikicin siyasar da Libiyan ke fama da shi.
Wata sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen kasar Aljeriya ta fitar, ta bayyana wannan ziyara a matsayin wata dama da Aljeriyar za ta yi amfani da ita, wajen jaddada goyon bayanta ga manufar wanzar da zaman lafiya, da tabbatar da cikakken ikon mulkin kan kasar ta Libiya.
Libiya dai ta tsunduma cikin yakin basasa, tun bayan hambarar da tsohon shugaban ta Muammar Gaddafi daga karagar mulki a shekarar 2011 da ta gabata.