Jami'an Tsaron Tunisia Tun Wargaza Wata Tawagan Yan Ta'adda A Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i15883-jami'an_tsaron_tunisia_tun_wargaza_wata_tawagan_yan_ta'adda_a_kasar
Jami'an tsaro a kasar Tunisia sun bada labarin wargaza wata tawagar yan ta'adda wadanda suke da aiki tare da kungiyar alqaeda, wadanda kuma suke shirin kai hare hare a wurare da dama a kasar
(last modified 2018-08-22T06:59:27+00:00 )
Dec 30, 2016 02:05 UTC
  • Jami'an Tsaron Tunisia Tun Wargaza Wata Tawagan Yan Ta'adda A Kasar

Jami'an tsaro a kasar Tunisia sun bada labarin wargaza wata tawagar yan ta'adda wadanda suke da aiki tare da kungiyar alqaeda, wadanda kuma suke shirin kai hare hare a wurare da dama a kasar

A bisa bayan da ministan cikin gida na kasar Tunisia ya bayar a jiya Alhamis, ya ce jami'an tsaron kasar sun kai sumame a wani wuria a garin Sousse kilomita 140 daga birnin Tunis babban birnin kasar, sun kuma kama mutane 10 wadanda sun tabbatar da cewa su yayayn kungiyar Alqaeda ta Okbatu bin Nafi ne. kuma shekarunsu ya kama daga 25-45 sannan akwai mata biyu daga cikinsu.

Majiyar ta fadawa tashar television ta Presstv a nan Tehran kan cewa yan ta'addan suna amfani da kafar sadarwa ta Telegrame wajen sadarwa a tsakanin yayan kungiyar a ciki da wajen kasar.

Gwamnatin kasar ta Tunisia dai ta bada labarin cewa a cikin wattan 10 na farko a wannan shekara ta wargaza tawagogin yan ta'adda kimani 160 a duk fadin kasar.