Jami'an Tsaron Tunusiya Sun Kame 'Yan Wata Kungiyar Ta'addanci A Kasar
Mahukunta a kasar Tunusiya sun sanar da cewa jami'an tsaron kasar sun sami nasarar kame 'yan wata kungiyar ta'addanci a yammacin kasar a ci gaba da fada da ta'addanci a kasar.
Rahotanni daga kasar Tunusiyan sun bayyana cewar a wata sanarwa da ma'aikatar cikin gidan kasar Tunusiyan ta fitar ta bayyana cewar jami'an tsaron kasar sun sami nasarar kame wasu mutane 10 'yan wata kungiyar ta'addancin nan ta 'Dakarun Uqbah bn Nafih' da ke gudanar da ayyukanta a kasar.
Sanarwa ta kara da cewar mutane goman da aka kama din 'yan shekaru 25 zuwa 45 ne kuma sun kumshi maza 8 ne da mata biyu.
Tsawon lokaci dai gwamnatin kasar Tunusiyan ta ba da himma wajen fada da ayyukan ta'addanci, to sai dai makwabtakar da take yi da kasar Libiya wacce a halin yanzu ta zamanto wata tunga ta 'yan ta'adda kana kuma da matsaloli na siyasa da kasar take fuskanta sun sa har yanzu kasar na ci gaba da fama da kutse na 'yan ta'adda.