Shugaban Burundi Yayi Barazanar Janye Sojojin Kasar Daga Somaliya
Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza yayi barazanar janye sojojin kasar daga cikin tawagar dakarun kungiyar Tarayyar Afirka da suke kasar Somaliya matukar dai ba a biya su albashinsu ba.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya bayyana cewar shugaba Pierre Nkurunzizan ya bayyana hakan ne yayin da yake korafin cewa sojojin nasa sun kai watanni 11 ba tare da albashi inda ya ce matukar dai ba a biya su ba, to kuwa zai janye sojojin nasa a watan Janairu mai kamawa.
Shugaba Nkurunzizan ya kara da cewa sojojin Burundin ba sun je kasar Somaliyan don neman kudi ba ne, face dai sai don taimakon kasar fada da 'yan ta'addan al-Shabab, to amma biyansu hakkokinsu wani lamari ne mai muhimmancin gaske.
Burundi dai wacce take da sojoji 5,400 ita ce kasa ta biyu, bayan kasar Uganda, wajen yawan sojojin tabbatar da zaman lafiya na Kungiyar Tararyar Afirka da suke kasar Somaliyan.