Kashi 60% Na Gabacin Birnin Musil Na Karshin Ikon Sojojin Iraqi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i15991-kashi_60_na_gabacin_birnin_musil_na_karshin_ikon_sojojin_iraqi
Wani babban komandan sojojin kasar Iraqi ya bada sanarwan cewa kashi 60% na gabacin birnin Musil yana karkashin ikon sojojin kasar da kuma masu goya masu bayan.
(last modified 2019-03-07T02:07:59+00:00 )
Jan 01, 2017 12:59 UTC
  • Kashi 60% Na Gabacin Birnin Musil Na Karshin Ikon Sojojin Iraqi

Wani babban komandan sojojin kasar Iraqi ya bada sanarwan cewa kashi 60% na gabacin birnin Musil yana karkashin ikon sojojin kasar da kuma masu goya masu bayan.

Tashar television ta Presstv ta nakalto Staff Lieutenant General Abdulwahab al-Saadi yan afadar haka a yau Lahadi ya kuma kara da cewa ko a yau sojojin kasar sun sami ci gaba a kwato yankunan ciki da kuma gewayen birnin na Musil, tungar yan ta'adda ta Daesh ta karshe a cikin kasar Iraqi.

Staff Lieutenant General Abdulwahab ya kara da cewa sojojinsa basa amfani da makaman gurneti a cikin birnin don kare fararen hulan da aka rutsa da su a cikin birnin daga mutuwa. Don haka ne aikin shiga birnin yake tafiyar hawainiya, amma dai ana samun ci gaba a duk rana.

Wani komandan sojojin kasar ta Iraqi ya bayyana cewa sojojinsa sun kashe yan ta'adda da dama a yakin da suka fafata a jiya Asabar sannan sojojin suna samun ci gaba zuwa tsakiyar birnin.

A ranar 17 ga watan Octoban da ya gabata ne sojojin kasar Iraqi da kawayensu suka fara kai farmakin kan birnin Musil daga arewacin kasar Iraqi don dawo da ikin gwamnatin kasar a birnin bayan ya fada karakshin ikon yan ta'adda a shekara ta 2014.