Aljeriya ta amince da warware rikicin kasar Syria ta hanyar lumana
Ma'aikatar harkokin Wajen Aljeriya ta amince da shirin warware rikicin kasar Aljeriya ta hanyar lumana.
Ma'aikatar harkokin Wajen Aljeriya ta amince da shirin warware rikicin kasar Aljeriya ta hanyar lumana.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Aljeriya Abdulaziz Bin Ali ya bayyana amincewar kasarsa da tsagaita wutar yakin da aka yi a kasar Syira sannan ya kara da cewa: Wajibi ne ga dukkanin bangarorin da su zama masu riko da zaman lafiya da lumana a matsayin hanyar da za ta ka ga warware rikicin kasar.
Bugu da kari, ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Aljeriya ta fitar da wani bayani da a ciki ta yi kira da a bude tattaunawa a tsakanin al'ummar kasar da zummar samun cikakken zaman lafiya.