Shugaban Kasar Sudan Ta Kudu Zai Kai Ziyarar Aiki A Kasar Sudan
Shugaban kasar Sudan ta kudu Silva keer zai kai ziyarar aiki kasar Sudan nan ba da dadewaba, inda ake saran matsalolin tsaro na yankin na daga cikin abubuwan da bangarorin biyu zasu tattauna.
Kamfanin dillancin labaran Chinhuwa na kasar China ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Sudan ta kudu Deng Alor yana fadar haka a jiya litinin ya kuma kara da cewa shugaba Silva kirr zai gana da shugaban kasar Sudan Umar Hassan El-bashir inda zasu tattauna batutuwa masu muhimmanci wadanda suka hada da batun yankin Abiye da suke takaddama a kan mallakarsa. Har'ila yau shuwagabannin biyu zasu tattauna batun ayyukan ta'addanci a kan iyakokin kasashen biyu.
Kasashen Sudan da Sudan ta Kudu sun rattaba hannu kan yerjeniyoyi don warware wadan nan matsaloli a cibiyar tarayyar Africa a birnin Adis ababa na kasar Ethiopia, amma sun kasa aiwatar da yerjeniyoyin a kasa.