Senegal Ta Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Matakin Bai Daya Kan Ta'addanci
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i1612-senegal_ta_bukaci_kasashen_duniya_su_dauki_matakin_bai_daya_kan_ta'addanci
Shugaban kasar Senegal ya yi kira ga kasashen duniya su dauki matsayi guda kan
(last modified 2018-08-22T06:57:54+00:00 )
Mar 03, 2016 07:04 UTC
  • Senegal Ta Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Matakin Bai Daya Kan Ta'addanci

Shugaban kasar Senegal ya yi kira ga kasashen duniya su dauki matsayi guda kan

Shugaban kasar Senegal ya yi kira ga kasashen duniya su dauki matsayi guda kan ayyukan ta'addanci a duniya. Maky Sall ya bayyana haka ne wa Jiridar الشرق الاوسط bugun London , ya kuma kara da cewa abinda muke ganin yake faruwa a gabas ta tsakiya bai takaita ga yankin kadai ba, amma yana da tasiri kai tsaye ga nahiyar Afrika.

Shugaban Senegal ya ce kungiyar Daesh barazana ce ga dukkan kasashen duniya don haka ya zama wajibi ga kasashen duniya su dauki mataki guda na kawo karshen ayyukan ta'addanci a duniya. Maky Sall ya ce gwamnatin kasar Senegala a shirye take hada kai da kasashen duniya musamman kasashen musulmi don yin wannan gagarumin aiki.