Wasu Mutane Sun Keta Alfarmar Masalalcin Simons Town A Afirka Ta Kudu
(last modified Sun, 08 Jan 2017 15:45:54 GMT )
Jan 08, 2017 15:45 UTC
  • Wasu Mutane Sun Keta Alfarmar Masalalcin Simons Town A Afirka Ta Kudu

Wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba sun keta alfarmar babban masallacin birnin Simons Town da ke kasar Afirka ta kudu.

Shafin yada labarai na News24 ya bayar da rahoton cewa, mutanen sun jefa naman alade da kazantar jikinsa gami da jininsa a cikin masallaci, matakin da ake ganin na tsokana ne.

Ghalib Jangar daya ne daga cikin musulmin yankin, ya bayyana cewa ga dukkanin alamu wadanda suka yi hakan suna da nufin tsokanar musulmi ne, amma kuma su ba za su tauki mataki na rashin tsari ba a kan wanna lamari.

Ita ma a nata bangaren babbar majalisar musulmin kasar Afirka ta kudu ta fitar da bayani, wanda a cikinsa ta yi Allawadai da kakkausar murya kan wannan mummunan aiki, tare da kiran musulmin yankin da su kwantar da hankulansu, kada su dauki wani mataki, domin kuwa majalisar tana bin kadun lamarin ta hanyoyin da suka dace.

Bayanin majalisar musulmin Afirka ta kudu ya ce musulmin kasar suna zaune da kowa lafiya  akasar, ga dukkanin alamu wadanda suka yi hakan sun shigo kasar ne da nufin haifar da wani rikici, wanda kuma musulmi ba za su taba fadawa cikin tarkonsu ba.

Yanzu haka dai an mika batun ga bangaren shari'a, yayin da jami'an tsaro kuma suka shiga gudanar da bincike.