Najeriya: An Kashe 'Yan ta'addar Boko Haram 15 A Jahar Yobe
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i16306-najeriya_an_kashe_'yan_ta'addar_boko_haram_15_a_jahar_yobe
Wasu 'yan kungiyar Boko Haram 15 Sun halaka bayan da sojoji su ka kashe su a wani yunkurin kai hari a jahar Yobe.
(last modified 2018-08-22T06:59:30+00:00 )
Jan 09, 2017 02:56 UTC
  • Najeriya: An Kashe 'Yan ta'addar Boko Haram 15 A Jahar Yobe

Wasu 'yan kungiyar Boko Haram 15 Sun halaka bayan da sojoji su ka kashe su a wani yunkurin kai hari a jahar Yobe.

Wasu 'yan kungiyar Boko Haram 15 Sun halaka bayan da sojoji su ka kashe su a wani yunkurin kai hari a jahar Yobe.

kamfanin dillancin labarun Reuters  ya ambato cewa;  An kashe 'yan ta'addar kungiyar ta Boko Haram ne a garin "Boni Yadi" da ke Jahar Yobe bayan da su ka yi kokarin kai hari akan wani sansanin soja a daren lahadi.

Bayan fada mai tsananin wanda ya ci rayukan sojoji biyar, yan kungiyar ta Boko Haram sun janye.

Sojojin Najeriya sun sanar da cewa; sun kori 'yan kungiyar ta Boko Haram daga cikin dajin Sambisa da ya zama tungarsu na tsawon  shekaru.

Hare-haren da kungiyar ta ke kai wa a yankin arewa maso gabacin kasar ya yi sanadin kwararar yan gudun hijira  a cikin gida da kuma waje, yayin da wasu da su ka kai  20,000 su ka kwanta dama.