An Tsige Ndume A Matsayin Shugaban Masu Rinjaye Na Majalisar Nijeriya
(last modified Tue, 10 Jan 2017 17:05:18 GMT )
Jan 10, 2017 17:05 UTC
  • An Tsige Ndume A Matsayin Shugaban Masu Rinjaye Na Majalisar Nijeriya

'Yan Majalisar Dattawan Nijeriya na jam’iyyar APC mai mulki a kasar sun tsige Sanata Muhammad Ali Ndume daga mukaminsa na shugaban masu rinjaye a majalisar inda suka maye gurbinsa da Sanata Ahmed Lawal.

Shugaban Majalisar Dattawan  Sanata Bukola Saraki ne ya sanar da hakan a yayin da yake karanta wasikar da 'yan jam'iyyar APC din suka aiko masa da ke kunshe da batun Sanata Ndume daga mukamin nasa na shugaban masu rinjaye a majalisar.

Har ila yau sanarwar ta bayyana Sanata Ahmed Lawan daga jihar Yobe a matsayin wanda zai maye gurbin Sanata Ndume a wannan matsayin.

A wata ganawa da yayi da manema labarai jim kadan bayan wannan sanarwar, Sanata Ndume ya bayyana tsananin mamakin da wannan matakin da aka dauka, wanda ya ce shi ba shi da masaniya kan kan dalilin da ya sanya 'yan majalisar suka dau wannan mataki.

Wasu kafafen watsa labaran dai suna ganin tsige Sanata Ndume din yana da alaka da maganganun da yayi ne yayin da 'yan majalisar suka zargi Sakataren gwamnatin tarayyar Nijeriya  Babachir Lawal da karbar rashawa da cin hanci da kuma kin tabbatar da Ibrahim Magu a matsayin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, wato EFCC, inda ya bayyana cewa majalisar dai ba ta zargi sakataren da cin rashawa ba kamar yadda kuma ba ta ki amincewa da Magu din ba, lamarin da ya sanya wasu 'yan majalisar mayar masa da martani.