Ma'aikatan Man Fetur A Tarayyar Nigeria Sun Fara Yajin Aiki
Ma'aikatan kamfanin man fetur da iskar gas a tarayyar Nigeria sun fara wani yajin aiki don tilastawa hukumomin kamfanin biyansu hakkokinsu.
Tashar television ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa ma'aikatan sun fara yajin aikin ne a jiya Talata, kuma ya zuwa yanzu an rufe bututan kwararar man fetur kimani 12 a yankin Niger Dalter, sannan akwai yiyuwan yawan wuraren da yankin aikin zai shafi ya kara fafada.
Wata majiya ta bayyana cewa mai yuwa yakin aikin ya kai ga kamfanin fidda iskar gas na Utorogu wanda zai iya shafar samar da wutan lantarki a duk fadin kasar.
Tarayyar Nigeria wacce ita ce tafi ko wace kasa hakkar man fitur da iskar gas a nahiyar Africa tana fama da matsaloli a bangaren haka da sarrafa man fetur da iskar gas ta yan ta'adda masu fasa bututan man a yankin Niger Dalter da kuma yaje yajen aikin ma'aikatan wannan bangaren.