Gambiya: Najeriya Na Tattauna Bai wa Shugaba Yahya Jammeh Mafakar Siyasa
Yan Majalisar Najeriya Suna Tattauna Yiyuwar Bai wa Shugaban Kasar Gambiya Takunkumin Siyasa
Yan Majalisar Najeriya Suna Tattauna Yiyuwar Bai wa Shugaban Kasar Gambiya Takunkumin Siyasa.
kamfanin Dillancin Labarun Fransa ya ambato Emmanuel Yisa Orker Jev, wanda shi ne shugaban kwamitin dokoki da kuma kasuwanci a majalisar dokokin kasar yana cewa; Bada mafakar siyasar ga shugaba Yahya Jammeh na kasar Gambiya yana a karkashin shirin tabbatar da zaman lafiya ne a kasar.
Jammeh wanda ya yi furuci da shan kaye a zaben shugaban kasar da aka yi a farkon wata Decemba 2016, ya lashe amansa ta yin kira da a sake yin bincike akan sakamakon zaben da ya baiwa Adama Barrow galaba.
Kasashen duniya da su ka hada da kungiyar tattalin arziki ta kasashen yammacin Afirka sun yi kira ga shugaban na Gambia da ya yi murabus cikin lalama ko ya fuskanci amfani da karfi.