Yan Bindiga Sun Kashe Jami'an Tsaron Masar A Yankin Kudancin Kasar
(last modified Tue, 17 Jan 2017 08:18:59 GMT )
Jan 17, 2017 08:18 UTC
  • Yan Bindiga Sun Kashe Jami'an Tsaron Masar A Yankin Kudancin Kasar

Wasu gungun 'yan bindiga sun kai wani mummunan hari kan wajen binciken ababan hawa da ke yankin kudancin kasar Masar, inda suka kashe jami'an tsaro akalla takwas tare da jikkata wasu na daban.

Tashar watsa labaran Sky News ta habarata cewa: Wasu gungun 'yan bindiga sun kaddamar da wani mummunan harin wuce gona da iri kan tawagar 'yan sandan Masar da suke gudanar da binciken ababan hawa a yankin garin Kharijah da ke lardin Wadi Jadid a shiyar kudu maso yammacin kasar a jiya Litinin, inda suka kashe 'yan sanda akalla takwas tare da jikkata wasu da dama.

Tuni dai jami'an tsaron kasar ta Masar suna fantsama sassa daban daban da suke yankin da nufin zakulo 'yan bindigan da suke da hannu a kai harin na jiya. 'Yan ta'addan kungiyar ta'addanci ta Baitu Maqdis da ke yankin Tsibirin Sina da ta shelanta biyayyarta ga kungiyar ta'addanci ta Da'ish suke daukan alhakin hare-haren wuce gona da irin da ake kai wa kan jami'an tsaron kasar a yankin na Tsibirin Sina.