Majalisar Kasar Gambiya Ta Tsawaita Wa'adin Mulkin Yahya Jammeh
Majalisar dokokin kasar Gambiya ta fitar da wani kuduri na tsawaita wa'adin mulkin shugaban kasar Yahya Jammeh har na tsawon watanni uku da zai fara daga yau Laraba 18 ga watan Janairun nan da muke ciki.
Gidan talabijin din kasar Gambiyan ne ya sanar da hakan a yau inda ya ce shugaban masu rinjaye na majalisar Fabakary Jatta ne ya gabatar da wannan kudurin a jiya Talata inda a yau kuma 'yan majalisar suka amince da shi.
Har ila yau kuma 'yan majalisar sun amince da dokar ta bacin da shugaba Jammeh ya kafa a jiya, kamar yadda kuma suka yi Allah wadai da abin da suka kira tsoma baki cikin harkokin cikin gidan da kungiyar Tarayyar Afirka (AU), Kwamitin tsaron MDD da kuma gwamnatin kasar Senegal suke yi.
Wannan mataki na majalisar dai yana zuwa ne kwana guda kafin asalin wa'adin mulkin shugaban Jammeh wanda ya sha kaye a zaben shugaban kasar yake karewa da kuma shirin da ake yi na rantsar da zababben shugaban kasar Adama Barrow da 'yan adawa suke cewa ba gudu ba ja da baya za a rantsar da shi a goben.