Magoya Bayan Harkar Muslunci Sun Bukaci A Saki Sheikh Zakzaky
Magoya bayan harkar muslunci a Najeriya sun gudanar da jerin gwano a birane daban-daban na Najeriya domin neman a saki Sheikh Ibrahim Zakzaky.
Kamfanin dillancin labaran Irna ya bayar da rahon cewa, magoya bayan harkar musluncin sun gudanar da jerin gwano ne domin kiran gwamnati da ta saki jagoran harkar muslunci a kasar (Islamic Movement) Sheikh Ibrahim Zakzaky, bayan da wa'adin da kotun tarayya da ke Abuja ta bayar kan a sake shi a cikin 45 ba tare da wani sharadi ba.
Wasu daga cikin kungiyoyin kare hakkin bil adama a Najeriya da ma wasu na kasa da kasa, sun bi sahun magoya bayan harkar musulunci, wajen kiran gwamnatin tarayyar Najeriya da ta mutunta dokar kasa, ta hanyar aiwatar da umarnin kotun tarayya.