Kame Tsoffin 'Yan Tawayen Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo A Kasar Uganda
(last modified Sat, 21 Jan 2017 05:54:48 GMT )
Jan 21, 2017 05:54 UTC
  • Kame Tsoffin 'Yan Tawayen Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo A Kasar Uganda

Rundunar tsaron Uganda ta kame tsoffin 'yan tawayen kungiyar M23 ta kasar Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo da suke cikin kasarta.

Rundunar tsaron Uganda ta kame tsoffin 'yan tawayen kungiyar M23 ta Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo da yawansu ya doshi 100 a kokarin da suke yi na kutsa kai zuwa cikin kasarsu. Wannan mataki na rundunar tsaron Uganda ya zo ne bayan da mahukuntan Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo suka yi zargin cewa: A kwanakin baya tsoffin 'yan tawayen kungiyar M23 karkashin jagorancin madugun kungiyar Sultani Makenga kimanin 200 sun kutsa cikin kasar Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo inda suka mamaye wasu yankuna a shiyar gabashin kasar.

A karkashin yarjejeniyar da aka cimma tsakanin mahukuntan kasashen Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo da na kasar Uganda tun a shekara ta 2013 tana kunshe da cewa: Tsoffin 'yan tawayen kungiyar M23 ta Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo da suka nemi mafaka a kasar Uganda dole ne su kunce damarar yaki, sannan ba su da hakkin komawa cikin kasarsu ta Dimokaradiyyar Congo.

Tun a watan Nuwamban shekara ta 2013 ne sojojin gwamnatin Jamhuriyar Dimokadiyyar Congo da taimakon dakarun wanzar da zaman lafiya da sulhu na Majalisar Dinkin Duniya suka murkushe 'yan tawayen kungiyar M23 lamarin da ya tilastawa daruruwan 'yan tawayen tserewa cikin kasar Uganda. A halin yanzu haka kuma mahukuntan Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo suna zargin cewa da hannun gwamnatin kasar Uganda a matakin da 'yan tawayen kungiyar M23 suka dauka na sake dawowa cikin kasarta dauke da makamai.

A gefe guda kuma a wani bincke da Majalisar Dinkin Duniya t gudanar yana nuni da cewa: Kasashen Uganda da Ruwanda ba su mutunta dokar hana aikewa da makamai ga 'yan tawayen Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, kuma suna ci gaba da gabatar da bayanan sirri gami da dabarun yaki ga 'yan tawayen kasar ta Dimokaradiyyar Congo, amma tuni mahuntan kasar Uganda suka yi watsi da wannan batu tare da bayyana shi a matsayin zargi maras tushe.

A fili yake cewa: Tashe-tashen hankula da suke faruwa a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo rigingimu ne da suka hada da na siyasa, kabilanci da kuma tsoma bakin kasashen waje a kokarin da suke yi na wawushe tarin dukiyoyin da Allah ya huwace wa kasar, kuma a halin yanzu haka mafi yawan yankunan da suke dauke da arzikin karkashin kasa a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo suna karkashin ikon 'yan tawaye ne lamarin da ke fayyace cewa: Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo tana cikin halin tsaka mai wuya.