A Yau Ne Ake Sa Ran Yahya Jammeh Zai Bar Kasar Gambiya
(last modified Sat, 21 Jan 2017 11:52:48 GMT )
Jan 21, 2017 11:52 UTC
  • A Yau Ne Ake Sa Ran Yahya Jammeh Zai Bar Kasar Gambiya

A wani lokaci a yau ne ake sa ran tsohon shugaban kasar Gambiya Yahya Jammeh zai bar birnin Banjul, babban birnin kasar ta Gambiya tare da shugaban kasar Guinea Alpha Conde don fara gudun hijira a wajen kasar bayan da ya amince zai sauka daga mulkin kasar.

A jiya Juma'a ne dai shugaba Jammeh ya amince ya sauka daga karagar mulkin kasar da kuma barin kasar bayan tattaunawa ta shiga tsakanin da ta gudana tsakaninsa da shugabannin kasashen Guinea Alpha Conde da na Mauritaniya Mohamed Ould Abdel Aziz wadanda suka tafi kasar don lallashinsa da ya amince ya sauka daga karagar mulkin.

Har ya zuwa yanzu dai ba a tabbatar da inda shugaba Jammeh din zai  tafi ba sai dai wani na kurkusa da sabon shugaban kasar Adama Barrow ya ce ana ci gaba da  tattaunawa dangane da yadda Jammeh din zai bar kasar da sauran batutuwan da suka shafi ficewar tasa.