Harin ta'addanci na Kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i17037-harin_ta'addanci_na_kungiyar_boko_haram_a_arewa_maso_gabashin_najeriya
Jami’an ‘Yan sanda a Najeriya sun ce mayakan Boko Haram sun shiga garin Askira Uba a Jihar Borno inda suka kashe mutane uku tare da sace mata bakwai
(last modified 2018-08-22T06:59:35+00:00 )
Jan 26, 2017 14:10 UTC
  • Harin ta'addanci na Kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya

Jami’an ‘Yan sanda a Najeriya sun ce mayakan Boko Haram sun shiga garin Askira Uba a Jihar Borno inda suka kashe mutane uku tare da sace mata bakwai

A wata sanarwa da ya fitar a wannan Alkhamis, Damian Chukwu babban Komishinan 'yan sanda na Jihar Borno ya ce mayakan Boko Haram sun kai wani mumunan hari a garin Dago na yankin Askira Uba inda suka kashe wasu Mutane uku tare da sace Mata Bakwai  sannan kuma suka cinnawa gidajen dake cikin kauyen wuta.

Kauyen Dago na kusa da garin Chibok inda mayakan na kungiyar Boko Haram suka yi awan gaba da 'yan Matan sakadare sama da 200 a watan Avrilu na shekarar 2014.

Kafin wannan hari dai, mayakan na Kungiyar Boko Haram sun yi awan gaba da wasu Mata kimanin 20 a wani kauye dake jihar ta Borno.

Hare haren ta'addancin da kungiyar Boko haram ke ci gaba da kaiwa a jihohin arewa maso gabashin Najeriya da kuma wasu yankuna na kasashen Camarou, Tchadi da Jumhoriyar Niger ya janyo asarar duban rayuwa tare da raba da milyoyin fararen hula da mahalinsu.