Matsalar Kudi Tana Barazana Ga Ci Gaban Ayyukan Kungiyar Tarayyar Afrika
Mataimakin shugabar kungiyar Tarayyar Afrika ya bayyana cewa: Matsalar karancin kudade na barazana ga ci gaba da gudanar da ayyukan kungiyar a fagen aiwatar da ayyukan dakarun wanzar da zaman lafiya da sulhu na kungiyar.
Erastus Mwencha mataimakin shugabar kungiyar tarayyar Afrika ta AU ya bayyana damuwarsa kan karancin kudade da ke addabar kungiyar tarayyar Afrika; Yana mai fayyace cewa: A halin yanzu haka kungiyar tarayyar Afrika tana fama da matsalar kudade da za a gudanar da ayyukan kula da dakarun wanzar da zaman lafiya da sulhu a wasu kasashen nahiyar Afrika musamman rundunar AMISOM da ke kasar Somaliya.
Erastus Mwencha ya kara da cewa: Matsalar ta samo asali ne daga karancin kudaden tallafi daga bangaren Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar tarayyar Turai.