Mayakan Boko Haram Sun Kashe Fararen Hula A Hanyar Maiduguri Zuwa Taraba
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i17171-mayakan_boko_haram_sun_kashe_fararen_hula_a_hanyar_maiduguri_zuwa_taraba
Sakamakon wani hari da mayakan Boko Haram suka kaddamar a kan fararen hula da ke kan hanyar Maiduguri zuwa jahar Taraba, inda suka kashe mutane tare da jikkata wasu.
(last modified 2018-08-22T06:59:36+00:00 )
Jan 30, 2017 09:27 UTC
  • Mayakan Boko Haram Sun Kashe Fararen Hula A Hanyar Maiduguri Zuwa Taraba

Sakamakon wani hari da mayakan Boko Haram suka kaddamar a kan fararen hula da ke kan hanyar Maiduguri zuwa jahar Taraba, inda suka kashe mutane tare da jikkata wasu.

Shafin Premium Times ya bayar da rahoton cewa, mayakan na Boko Haram sun tare hanyar Maiduguri - Biu wadda ita ce babbar hanyar zuwa jahar Taraba daga birnin na Maiduguri, inda suka bude wuta kan fararen hula matafiya.

Rahoton ya kara da cewa akalla mutane 7 ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon harin, da suka hada da wasu daliban jami'ar Maiduguri da suka kammala karatu, yanzu haka kuma wasu daga cikin wadanda suka samu munanan raunuka sakamakon hari suna kwancea  asibiti.