Sojojin Najeriya sun tsarkake wasu tungogin mayakan boko Haram
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i17279-sojojin_najeriya_sun_tsarkake_wasu_tungogin_mayakan_boko_haram
Sojojin Najeriya sun sanar da tsarkake wasu wuraren kungiyar boko haram a Jihar Borno
(last modified 2018-08-22T06:59:37+00:00 )
Feb 02, 2017 14:11 UTC
  • Sojojin Najeriya sun tsarkake wasu tungogin mayakan  boko Haram

Sojojin Najeriya sun sanar da tsarkake wasu wuraren kungiyar boko haram a Jihar Borno

A cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Alkhamis, Kakakin rundunar Sojin Najeriya  Kanal Sani Usman Kuka Sheka ya ce Sojojin kasar sun samu nasarar tsarkake wasu tungogin mayakan kungiyar boko haram uku a yankuna daban daban na Jihar Borno dake shiyar arewa maso gabashin kasar.

Sanarwar ta kara da cewa a yayin wannan sumame, Sojojin sun samu nasarar hallaka mayakan kungiyar ta boko haram uku tare da jikkata wasu da dama na daban, saidai a nasu bangare su ma sojojin sun yi asarar mutanan su uku.

Dakarun tsaron Najeriyan na ci gaba da karfafa matakan tsaro a arewa maso gabashin kasar da kuma kan iyakokin kasar da suka danganta da kasashen Tchadi, Nijer da Kamaru a wani mataki na kokarin kawar da kungiyar Boko Haram.

Alkaluma na cewa daga lokacin da kungiyar Boko haram ta fara kai hare haren ta'addanci a shekarar 2009, sama da Mutane dubu 20 ne suka hallaka yayin da wasu kimanin million biyu da dubu dari uku na daban suka rasa mahalinsu.