An Kashe Sojojin Mali Hudu A Arewacin Bamako
Feb 04, 2017 07:14 UTC
Rahotanni daga Mali ne cewa sojojin kasar hudu ne suka rasa rayukansu a wani hari da aka kai kan sansaninsu dake a yankin Menaka a arewacin kasar.
Da yake tabbatar da hakan ga kanfanin dilancin labaren AFP wani kwamandan soji ya ce an kai harin ne da sanyin safiyar yau, inda aka kashe sojojin kasar hudu.
Majiyar ta kara da cewa an kashe wani adadi mai yawa na 'yan bindigan, da har yanzu ba'a san ko suwa ne ba.
Bayanai sun ce 'yan bindigan sun zo ne da muggan makamai, kuma tuni sojojin kasar suka shiga biyar sahunsu.
Arewacin kasar mali dai ya jima yana fama da matsalar mayakan jihadi.
Tags