An tsawaita aikin Dakarun Masar a kawancen Saudiya
Shugaban kasar Masar ya tsawaita aiyukan Sojojin kasar sa a harin wuce gona da iri kan kasar Yemen kalkashin Jagorancin masarauta Ali-sa'oud
Tashar telbijin din CNN ta habarta cewa a wannan Lahadi, Fadar Shugaban kasar Masar ta sanar da cewa Majalisar tsaron kasar bisa Jagorancin Shugaba Abdulfatah Alsese ta amince ta tsawaita zaman Sojojin kasar cikin kawancen Saudiya a hare-haren wuce gona da irin da suke kaiwa kan Al'ummar kasar Yemen.
Tun daga Watan Maris din 2015 ne kasar ta Saudiya bisa goyon bayan kasashen Amurka da Burtaniya ta fara kai hare-haren wuce gona da iri kan Al'ummar kasar Yemen da nufin mayar da Shugaban kasar da ya yi murabus Abdu Rabbahu Mansur Hadi kan karagar milki, lamarin da ya yi sanadiyar shahadar dubun dubatan fararen hula tare da rusa kasar.
Duk da irin da'awar da kasashen Yamma ke yi na kare hakin bil-adama, amma har yanzu sun ki su dauki mataki na hana saudiyan ci gaba da kasashen fararen hula a kasar ta Yemen du kuwa da cewa kungiyoyin kare hakin bil-adama na Duniya sun yi ta kiraye kiraye dangane da wannan batu.