An Sace Wata Malamar Addini 'Yar Kolumbia A Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i17443-an_sace_wata_malamar_addini_'yar_kolumbia_a_mali
Rahotanni dake cin karo da juna a Mali na cewa wasu 'yan bindiga sun sace wata mallamar addini 'yar asalin kasar Kolumbia a kudancin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:39+00:00 )
Feb 08, 2017 07:44 UTC
  • An Sace Wata Malamar Addini 'Yar Kolumbia A Mali

Rahotanni dake cin karo da juna a Mali na cewa wasu 'yan bindiga sun sace wata mallamar addini 'yar asalin kasar Kolumbia a kudancin kasar.

Wata majiyar soji da ta tabbatarwa da kanfanin dilancin labaren AFP hakan ta ce an sace malamar ne a cikin daren jiya Talata a kusa da garin Kuntila dake nisan kilomita 400 daga Bamako babban birnin kasar.

Tuni kuma a cewar majiyar sojojin kasar suka bi sahun 'yan bindigan.

Malamar wace ba'a bayyana sunan ta ba na aiki ne a cocin garin na Kuntiala, kuma har lokacin fasara wadanan labaru babu wata kungiya data dau alhakin sace ta.