MDD: Har Yanzu Gwamnatin Burundi Tana Take Hakkokin Bil Adama
(last modified Wed, 08 Feb 2017 20:21:06 GMT )
Feb 08, 2017 20:21 UTC
  • MDD: Har Yanzu Gwamnatin Burundi Tana Take Hakkokin Bil Adama

Majalisar dinkin duniya ta zargi gwamnatin kasar Burundi da ci gaba da take hakkokin bil adama da kuma kuntata wa 'yan siyasa masu adawa da gwamnatin kasar.

Shafin yada labarai na Afrik Time ya bayar da rahoton cewa, jami'in majalisar dinkin a kan kare hakkokin bil adama Michel Forst ya bayar da rahoto ga majalisar kan halin da ake ciki a kasar Burundi, inda rahoton nasa ya yi nuni da cewa har yanzu gwamnatin kasar tana ci gaba da cin zarafin jama'a saboda dalilai na siyasa.

Majalisar dinkin duniya ta sanar da cewa za ta mika rahoton na Michel Forst ga kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar, kuma za a karanta rahotona  zaman da kwamitin zai gudanara  cikin Maris a birnin Jeneva na kasar Switzerland.