An Cafke Mutune Biyu Bayan Sace 'Yar Kolumbia A Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i17471-an_cafke_mutune_biyu_bayan_sace_'yar_kolumbia_a_mali
Hukumomi a Mali sun ce an cafke mutune biyu da ake zargi da hannu a sace wata malamar addini 'yar asalin kasar Kolumbia a kudancin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:39+00:00 )
Feb 09, 2017 02:20 UTC
  • An Cafke Mutune Biyu Bayan Sace 'Yar Kolumbia A Mali

Hukumomi a Mali sun ce an cafke mutune biyu da ake zargi da hannu a sace wata malamar addini 'yar asalin kasar Kolumbia a kudancin kasar.

Malamar mai suna Gloria Cecilia Narvaez Argoti, 'yar kimanin shekaru 50 an dai sace ta ne a cikin daren Talata data gabata a garin Kuntila.

Har kawo yanzu dai babu wata kungiya data dau alhakin sace matar, wace tuni aka fara zargin mayakan jihadi da sace ta.

Wata majiyar soji da ta tabbatarwa da kanfanin dilancin labaren AFP hakan ta ce wasu mutane hudu ne suka sace malamar a kusa da garin na Kuntila dake nisan kilomita 400 daga Bamako babban birnin kasar, inda tuni sojojin kasar suka bi sahun 'yan bindigan.

Sacewa ko garkuwa da mutane musamen turawa ba sabon abu ne ba a Mali, inda ko a ranar 24 ga watan Disamba bara wasu 'yan bindiga suka sace wata 'yar asalin kasar Faransa mai suna Sophie Pétronin a birnin Gao dake arewacin kasar.