Sudan Ta Kudu: Bullar Sabuwar Kungiyar 'Yan tawaye.
Wata Kungiyar 'yan tawaye mai dauke da makamai ta bulla a yankin Equatorial a kasar Sudan ta kudu.
Wata Kungiyar 'yan tawaye mai dauke da makamai ta bulla a yankin Equatorial a kasar Sudan ta kudu.
Mai shiga tsakani a rikicin gwamnati da 'yan tawaye a kasar ta Sudan ta kudu, wato tsohon shugaban kasar Botswana, Festud Mogae, ya fadawa kafar watsa labaru ta Africa Times labarin bayyanar sabuwar kungiyar mai dauke makamai, ya ci gaba da cewa: Abinda hakan ya ke nufi shi ne kara watsuwar rashin tsaro a cikin kasar wanda ko kadan ba a maraba da shi.
Festus Mogae, ya ci gaba da cewa; Da akwai rahotanni da su ke nuni da cewa sabuwar kungiyar tana kai wa 'yan kabilar Dimka hari wacce daga cikinta ne shugaba Silva Kiir ya fito, kuma suna aikata laifukan yaki.
Gabanin wannan lokacin, gundumar ta Equtatorial ba ta fuskanci tashin hankali ko fada a tsakanin sojojin da su ke goyon bayan shugaba Silva Kiir da tsohon mataimakinsa, Reik Machar ba.