Rigingimin Kabilanci A Arewacin Kasar Mali Sun Janyo Kisan Mutane Akalla 13
Rikicin kabilanci tsakanin Fulani makiyaya da kuma yan kabilar Bambara a tsakoyar kasar Mali ya jawo mutuwar mutane akalla 13 tare da kona gidaje da dama.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto wani jami'in ma'aikatar cikin gida na kasar yana fadar haka ya kuma kara da cewa tun ranar lahadin da ta gabata ne aka fara fada tsakanin yan kabilar bambara wadanda sune mafi rinjaye a kasar tare da kabilar fulani makiyaya.
Wani ba fulatani mai suna Modibo Dicko kuma shugaban kungiyar kare hakkin dan'adama na Fulani ya shaidawa reuters cewa fadan ta tashi ne bayan kisan wani dan kabilar Bambara a kusa da garin Macina kilomita 300 daga birnin Bamako, bayan haka ne yan kabilar Bambara suka farwa Fulanin da suke tuhuma da kashe mutuminsu. Dicko ya ce an kashe mutane 45 kuma an kona gidaje da dama na kabilan fulani a yankin.